Monday 24 March 2008

RAHOTON TARON MARUBUTA NA KASA DA KASA MASU RUBUTU DA HARSHEN GIDA

Daga Sharfaddeen Sidi Umar

KUNGIYAR Marubuta ta Nijeriya (ANA) reshen jihar Sokoto ta shirya kuma ta karbi bakuncin marubuta da suka fito daga jihohin Kano da Katsina da Kebbi da Zamfara da Abuja da kuma jamhuriyar Nijar, wanda aka yi a babban birnin jihar sokoto, a ranakun 27 ga Fabrairu zuwa 1ga Maris 2008.
Kamar yadda aka tsara mahalarta taron sun iso Sokoto a ranar 27 ga watan Fabrairu aka saukar da su a masaukin baki na University Guest Inn,bayan hutawar bakin sai aka kai ziyarar ban girma ga gwarzon marubuci kuma fasihin mawaki, tsohon shugaban kasa a jamhuriya ta farko, Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari, Turakin Sokoto, inda ya nuna murnar sa da jin dadinsa kan wannan ziyarar ta tarihi da aka kawo masa, ya kuma yi kira ga marubuta da su kara zare dantse ga yin rubutu mai ma'ana.Ya karanta wakarsa ta Nijeriya, aka kuma dauki hotuna da tsohon shugaban kasar.
A rana ta biyu ranar bude taro an yi bikin bude taron ne a mazaunin cikin gari na jami'ar Usumanu Danfodiyo a babban dakin taro na mazaunin cikin gari na jami'ar da ke kusa da Cibiyar Nazarin Hausa. An fara taron ne da karfe 11 na safe, Sanata Mukhtar Abdulkarim wanda ya ke fitaccen marubuci ne ya zama shugaban taron, ya yin da sauran manyan baki suka hada da Dr. Bala Muhammad shugaban Hukumar A Daidaita Sahu ta jihar Kano wanda ya gabatar da mukala ta farko da Dr Nuhu wanda ya wakilci shugaban jami'ar Usmanu Danfodiyo da Malam Aminu Musa, Mataimakin Darakta a Hukumar Tace Fina-finai ta jihar Kano wanda kuma ya wakilci shugaban hukumar Malam Rabo da kuma Khadi Ahmad Alkali Bello Gidadawa, wanda ya wakilci mahaifinsa, Dan Galadiman Waziri, Alkali Bello Gidadawa da kuma Mashahurin mawaki, Malam Sambo Wali.
Tun da farko, Kabir Assada, shugaban kungiyar marubuta ta kasa, reshen jihar Sokoto, ya yi jawabin maraba, inda ya yi tsokaci akan yadda wannan taron ya samo asali tun a shekarar 2006 inda aka yi taron farko a jamhiriyar Nijar. Ya yi fatar za a yi taro lafiya a kare lafiya.
Da yake jawabi, shugaban taro Sanata Mukhtar Abdulkarim ya yi tsokaci sosai kan rubutu da alfanunsa ga al'umma da irin baiwar da marubuci ya ke da ita. Shi kuwa Dr Bala Muhammad ya yi kalamai masu ratsa zukata, ya ce a dinga yin rubutu mai ma'ana saboda a cewar sa akwai gasar da aka shirya kwanan baya a Abuja don karrama wani marigayi, amma kuma ya ce “littafin da ya zo na daya ba a iya tafiya da shi a karanta shi a gaban kabarin mamacin.” Ya kara da cewa marubuta su karkata rubutun su akan abin da al'umma za su amfana. “A dinga rubutu wanda mutun zai iya karantawa ko a gaban gyatumarsa. Ya nuna ka da marubuci ya yi rubutu don neman suna, sai domin burin ganin ya inganta rayuwar al'umma ta hanyar ilmantarwa da nishadantarwa, idan sunan ya samu ba laifi, sai a godewa Mahalicci.
Daga nan sai fitaccen mawaki Sambo Waliyi ya gabatar da wakensa mai taken “Kasidar Zaman Banza” ya birge mahalarta taron matuka,
Daga nan kuma sai Dr. Ibrahim Malumfashi ya yi jawabin godiya ga mahalarta taron musamman ga Jami'ar Danfodiyo wanda ta bada gudunmuwa gwargwado domin ganin wannan taron ya yi armashi. Daga nan aka tashi aka raka shugaban taron. Bayan tafiyarsa taron ya ci gaba inda fitaccen marubucin wasan kwaikwayo Hadi Abdullahi Alkanci ya gabatar da mukalar sa mai taken “Wasan Kwaikwayo Na Hausa: Ga koshi Ga Kwanan Yunwa” A ciki ya ce akwai bukatar kafa cibiyar nazarin hausa mai zaman kanta ba ta gwamnati ba. Ya yi fashin baki sosai kan wasan kwaikwayo, ya kuma nuna ana yi wa Hausa dariya saboda ba ta iya baza kimiyya da fasaha ba, sai nishadi da raha, ya nuna cewar duk lokacin da marubuci ya dauki alkalaminsa ya tuna shi fa Musulmi ne kuma bahaushe ta hakan zai fahimci yadda zai siffanta labarinsa. Ya kara da ce wa a yanzu wasan kwaikwayo bai samu tagwomashi kamar 'yan uwan sa ba. Daga nan Dr. Malumfashi ya tashi inda ya nuna wasan kwaikwayo matukar bai shiga cikin manhajar ilimi ba, to, an yi kamar ba a yi ba ne, ya nuna aiki ne ja wurin marubuta wasan kwaikwayo don za a iya shekara ana rubutawa amma kuma ba za a iya samun abin da ake so ba. Ya nuna yana son Balaraba Ramat, Ado Gidan Dabino da Sa'adatu Baba Ahmad su yi rubutu kan wasan kwaikwayo. Dr. Malumfashi ya nuna ana da littattafan Hausa 1,886 cikinsu 400 na mata ne yayin da 26 kacal suke na wasan kwaikwayo.Wanda ya rubuta wasan kwaikwayo na farko shi ne Alhaji Abubakar Tunau Kayayen Sardauna a 1949.
An tashi taron da karfe 1:40 aka koma masaukui aka yi salla aka ci abinci. Tahir Fagge wanda yake zaune a Sokoto ya zo masaukin bakin ya yi barka da zuwa ga mahalarta taron.
Da karfe biyar an kai ziyara a Hubbaren Shehu Danfodiyo, aka zagaya kabarinsa, da na sauran sarakunan Musulunci da waliyyai, an dauki hotunan tarihi a hubbaren.
Daga nan aka kai ziyarar ban girma ga kakan mawaka kuma shugaban kungiyar marubuta da manazarta wakokin Hausa ta Nijeriya Alkali Bello Gidadawa [an Galadiman Waziri mai shekaru 99. Yayi maraba da baki, ya yi addu'ar samun ci gaba a rubutun Hausa. Daga nan aka koma masaukin baki, aka ci gaba da taron a dakin taron masaukin bakin inda 'yan kungiyar chanis karkashin jagorancin Buhari A.Dagara wanda aka fi sani da Masta Alko suka nishadantar da mahalarta taron. Bayan su 'yan dandalin nishadi sun cashe da wakar Nijeriya da Nijar ta Fati Nijar, an kuma yi diramar dandali karkashin shiryawar Hadi Abdullahi Alkanci.
Da karfe 10:20 aka bude fagen karatun kananan labarai da wakoki, aka soma da
1-Lawal Adamu Giginyu “Soyaya ko Zamba Cikin Aminci” - Wake
2-Rabi'u Na'auwa” Wanene Masoyi” - Tsakure daga wani littafi nasa
3-Sule Maje Rejeto “Gidan Mace” Tsakure daga wani kagaggen labarinsa
4-Ali Liman “Da kyar Na Sha” Gajeren Labari
5-Kabir Assada “Ba suna” amma Gidan Dabino ya ce labarin ya dace a ce masa “Mace? “
6-Ado Gidan Dabino “So ya cika” labari
7-Dr malumfashi “Zamba Ba Ta karewa” labari
8-Usman Buhari Sani “Aljannar Masa” labari
9-Maryam Ali Ali “Bacin Rana” tsakure
Daga nan aka yi tambayoyi da muhawarori masu zafi musamman ga Malumfashi akan ra'ayinsa na cewa bai yarda akwai so ba. An fafata sosai kan wannan, kai ya dau zafi, cikin wadanda su kalubalanci Malumfashi akwai Hadi Abdullahi Alkanci wanda musamman ya rubuta littafin martani mai suna “Shin So Gaskiya Ne?” Sanadiyar makalar Malumfashi mai taken “So Hawainiya ko Dala” wacce ya gabatar shekaru sha wani abu da suka wuce, a cewar Malumfashi har yanzu dai ba a ba shi amsa ba, kuma ko da an ba shi bukatar sa ta biya tun da an yi nazarce-nazarce da dama kanta. An tashi taron da karfe 12:14 na dare. Anan aka raba tikitin cin abincin safe saboda masu bukatar karyawa da wuri.
Washe gari juma'a wacce aka mayar ranar karshe an bar masaukin baki aka ziyarci gidan ajiye kayan tarihi da al'adu na Waziri Junaidu da ke unguwar Rogo da sanyin safiyar juma'ar, mukaddashin Darakta ne ya tarbi marubutan, ya zagaya da su bangarori hu]u daga cikin bangarori biyar da ake da su a wannan hukumar. Marubuta sun debe keyar ido da abubuwa da dama na tarihin Daular Usmaniyya, an dauki hotona a wurin. An bar gidan tarihin wanda aka kafa a 1973 zuwa gidan Sanata Muktar Abdulkarim da ke unguwar Guiwa da karfe 12:44. Sanatan ya yi maraba da baki cikin harshen faransanci, ya kuma bayyana wuyar da marubuta ke sha wurin rubuta littaffai, ya ce sau da yawa za ka rubuta littafi ka bayar a duba ma, wanda ka baiwa ya ki dubawar, karshenta ma ya salwanta, ya bayar da misali da Babban littafin Tanko Yakasai wanda ya bata baki daya wajen dubuwa, ya nuna sam! ka da marubuci ya dauki rubutu a matsayin sana'a. Sanatan ya karanta wakar “The Governor” ta cikin littafnsa na “The Book of Poems For Inspiration” daga nan aka yi karance-karance.
1- Ali Liman “My magic for the temtrim.”
2-Gidan Dabino “Ba suna” Sanatan ne ya wake
3-Muh'd Kabir Sani Katsina “Na yi musabaha da shugaba kasa” Labari
4-Halima Sarmai “Ba suna” Labari
An bar gidan Sanata bayan da aka jika makoshi, aka wuce masallacin juma'a daga can aka koma masauki aka yi kalacin rana, aka huta aka ci gaba da taro da karfe biyar na yamma. Nasir Wada Khalil ya gabatar da takardarsa mai taken Hikima kayan mumini:Tsokaci kan Alkali Bello Gidadawa da bargonsa na hikima. Ya yi jawabi sosai wanda ya ja hankalin jama'a sosai, daga nan Shaihin Malamin jami'ar Danfodiyo kuma shugaban kwalejin ilimi ta Shehu Shagari SSCOE Farfesa A. B. Yahaya ya gabatar da mukalar sa mai taken “Marubucin Wakokin Hausa” in da ya yi bayani sosai kan waka da amfaninta ga al'umma, da irin salon da mawaki ya kamata ya yi amafani da shi, inda ya kawo misali da fitacciyar wakar “Sakkwatawa suna bayanka” ta Bashir Dandago wacce har yanzu wasu ke ]aukar Farfesan ne ya rubuta ta duk da ya ce ba shi ba ne. An yi tambayoyi da sharhi ga bayanan Farfesan, aka tashi karfe bakwai, aka je aka yi salla aka yi kalacin dare aka dawo dakin taro da karfe tara inda Sambo Waliyi ya karanta tarihin Shehu Danfodiyo ya kuma yi wasu wakokin. An shiga zagaye na biyu inda aka soma karatun labarai da wakoki kamar haka:
1-Sa'adatu Baba Ahmad “Duhun Dare” Tsakure
2-Binta Rabi'u Spikin “Dabaibayi” Tsakure
3-Nasiru Bello “Lamarina” Labari
4-Rabi'a Talle Mai Fata Jos “Ba ni ya fi so ba.” Labari
5-Ado Gidan Dabino “Kwauron Baki” Labari
6-Rabi'u Na' auwa “Haduwar so ko takaici?” Wake
7-Maryam Ali Ali “'Yar baiwa” Labari
8-Hafsatu Abdulwahid “Alkali mai ilimi, mai basira” Labari
Daga nan aka yi tambayoyi da caccaka mai zafi. Sai 'yan Nijar su ka yi wasan kwaikwayo biyu wadanda suka kayatar matuka.
Hadi Abdullahi Alkanci ya yi tsokaci kan fitaccen littafin nan “Mace Mutum” inda ya nuna mamakinsa kan ba wanda ya ce uffan kan littafin, ya bayyana zai yi littafi cikin littafin Mace Mutum, wato rayuwar mace karkashin jahilci da ilimin boko, ya ce Fatima Godiya ta gamu da bala'i 12, Amina ta gamu da 7 a cikin littafin, daga karshe ya yaba wa marubuciyar kan hikima da hazaka da kwatance da take da shi.
A zagaye na biyu an gabatar ta ka'idojin rubutu, gajerun labaru da wakoki kamar haka:
1-Abdullahi Shu'aibu Gwabza “ka'idojin Rubutu”
2-Salmu Hassan “Yi wa namiji tabewa ne” Labari
3-Hajiya Mimi “Ta'aziyar Sultan Maccido” Waka
4-Sule Maje “Ramuwa ko Adalci” Labari
5-Buhari Dagara “Hanyar mikiya” Tsakure
6-Idris Aliyu Daudawa “Duniyar nan” Wake
7-Alhassan Ahmad Ikiyu “Ba suna” labari da wake
8-Sharfaddeen Sidi Umar “Rabuwa” Labari
9-Mamman Sahabi “Ba suna” Labari
An yi tambayoyi da muhawarori aka kuma raba satifiket ga mahalarta taron da littattafan turanci Gone beyond redemption, The man who have failed, The book of poems for inspiration, da The poems for the new generation wadanda Sanata MukhtarAbdulkarim ya bayar da dabinon da Alkali Bello ya bayar.
Shugaban ANA na Katsina, Alhaji Muhammad Kabiru Sani ya bayar da sanarwar za a yi taron na gaba a Katsina a karshen wannan shekarar, kasancewar wannan taron da aka yi a watan Disambar bara ya kamata a yi shi. Za a yi taron na Katsina bayan babban taron ANA da za a yi a Zamfara a watan Nuwanba.
An yi addu'o'in kammala taron lafiya cikin murnar nasarar da taron ya samu an tashi da karfe biyun dare.
Tuni dai har mahalarta taron sun koma garuruwansu lafiya.

Monday 29 October 2007

Daga kin gaskiya...

Daga
Isah M. Bello Na’iyya

Ban cika son in tabi abinda ya shafi jama’a ba, don gudun kar in yi wa wani ba daidai ba, amma kuma duk da haka, da yake masu magana na cewa gyara kayanka bai zama sauke mu raba, ina ganin tilas in ce wani abu.
Hausawa ke cewa, daga kin gaskiya sai bata, mai karatu, sanin ka ne cewa duk fa yadda aka narka karfe sunansa karfe, na fahimci saboda haka ne ma ake kwatanta gaskiya da dokin karfe, ko tana gudu kama ka haye, ba ka faduwa insha Allahu.
Dukkan lamari ko sha’anin da mutum zai aikatawa a rayuwarsa, indai yana bukatar ci gaba da kuma nasara, to tilas sai ya gama da gaskiya. Gaskiya ita ce takobin yakin duk wani lamari na rashin gaskiya ko yaudara ko zalunci ko ha’inci da ya addabi jama’a.
Babu wai wai, domin gaskiya ita ce addinin mutum, kuma da ita ce bawa zai yi godogo ko tinkaho, har ya zuwa karshen rayuwarsa. Bari in baka misali, - idan kai dan kasuwa ne ko ma’aikacin gwamnati, mai mulki ne kai ko mai sarauta, kai attajiri ne ko talaka, kai ko ma dai wane irin matsayi ka tsinci kanka a rayuwarka ta duniya, sai ka zamo mai gaskiya sannan mutane za su soma tunanin cewa kai mutum ne kammalalle kuma mai ma’ana, mai adidni, gwarzo kuma haziki.
Gaskiya ce kurum za ta iya sanya ka zamo sananne a cikin al’umma wanda kuma ake alfahari da shi. Kar ka manta da duk lokacin da gaskiyar mutum ta yi kadan to fa tabbas abokan huldarsa ma za su yi karanci.
Kar kuma ka manta duk fa wanda karya ta hada ku, to gaskiya za ta raba ku, amma idan gaskiya ce ta hada ku, to karya ba ta isa ta raba ku ba. sau da yawa rayuwarka za ta baci idan kuna magana da wani, to sai dai kuma kai tsaye kana iya fahimtar cewa gaskiya ce yake fada ma domin maganar gaskiya ba ta yi kama da kowace irin magana ba.
Haka kuma, a duk lokacin da aka fada ma maganar gaskiya, ka daure ka dauke ta ke kuma kar~eta hannu biyu, ka yi aiki da ita, insha Allahu za ka ji da]in tafiyar da rayukarka. Kowane al’amari yana karfafa ne idan aka yi aiki da gaskiya a cikinsa.
Dan uwa, mai karatu, ka taba aikata gaskiya? An taba yin aikin gaskiya a tare da kai? Ka taba ganin mutumin da gaskiyar sa ta kare? Ka taba jin kana kyamar mutumin da ke fadin gaskiya? Da yawa na san akwai dimbin tambayoyin da watakila za ka iya amsawa a game da kanka a kan mai gaskiya da maras gaskiya.
Hausawa kan yi wa gaskiya kirari iri-iri kamar: gaskiya mai daci, gaskiya ba ta neman ado, gaskiya matakin nasara, gaskiya dokin karfe, gaskiya mai dadi ko an ki ta ana ganin ranar ta, kowa ya ki gaskiya rabo nai kunya, in za ka fadi fadi gaskiya, komai ta ka ja maka ka biya.
Lokaci da yawa fadin gaskiya, yakan jayo wa mutum fitina, amma in ya yi hakuri zai ga amfanin fadin gaskiyar ko da kuwa akan sa ne.
Bari in baka wani dan takaitaccen labari game da wani bawan Allah, wanda labari ne mai karantarwa.
Wata rana wani bawan Allah yana cikin karantarwa a kofar gidansa, sai ga wani barawo a guje, yana gudu yana neman agaji daga wadanda suka biyo shi, yana zuwa wurin wannan bawan Allah, sai ya ce don Allah Malam ka taimake ni ka da su kashe ni, sai malamin ya ka da baki ya ce, ga wundi nan ka dauka ka boye kanka, barawon kuwa bai yi wata-wata ba ya dauki wundin ya zagayawa kansa ya boye, can kuma sai ga wadanda suka biyo shi, su ma suna zuwa sai suka cewa malamin don Allah malam barawo ne muka biyo ya bace muna, don Allah ina ka ga ya bi sai Malamin ya ce ga shi nan cikin wundi, nan take mutanen suka fusata suka yi gaba suna fada suna cewa ya ya za mu ce ma muna neman barawo ka ce wai ga shi nan cikin wundi, wane irin wundi? Bayan sun wuce sai barawon ya fito daga cikin wundin yana cewa hakika ko gobe gaskiya na aiki, kuma tun daga wannan lokacin barawon nan bai sake yin sata ba.
Dan uwa mai karatu, idan har za ka yi duba mai kyau na nazari, to, za ka fahimci cewa addinin Musulunci ma an gina shi baki dayan sa a kan gaskiya. A duk tsawon rayuwarka kuwa, matukar aka san ka da rashin gaskiya to, a wasu lokuta ko da gaskiya ka yi ba a yarda da kai.
A cikin Alkur’ani Mai girma, Allah Madaukakin Sarki Yana cewa, “ku fadi gaskiya daga Ubangijinku, amma idan kuka ga dama ku yi imani, idan kuka ga dama ku kafirce.”
A wata ayar kuwa Allah Yana cewa, “ya ku wadanda suka yi imani, ku ji tsoron Allah ku kasance masu gaskiya.”
A cikin wani Hadisi, Manzon Allah (SAW) ya na cewa, ita gaskiya tana shiryawa zuwa ga aljanna. Har wa yau dai Manzon Allah (SAW) yana cewa a cikin wani hadisi, cewa “na hore ku da yin gaskiya, hakika ita gaskiya tana tare da da’ar Allah dukkan su kuma suna kai mutum aljanna.”
Allah ya taimakemu mu zamao masu gaskiya amin summa amin.

Sunday 19 August 2007

Me PDP Ke So?

PDP fawa!, PDP fawa!!, Wannan shi ne kirarin jam’iyyar PDP, jam’iyyar siyasa mafi girma a nahiyar Afurka! Haka ne mana, domin kullum haka suke fada! Ita dai jam’iyyar PDP, ita ce ke jan ragwamar mulkin gwamnatin tarayyar Nijeriya da kuma mafi rinjayen jihohi 36 a Nijeriya. Jam’iyya ce da ta hada tsofaffi da sababbin jinin ‘yan siyasa, jam’iyya ce da ke alfahari da tattara tofaffi da kuma manyan sojojin da ma tsofaffin shugabannin kasar nan. PDP ke nan, jam’iyyar da ta taushe sauran kananan jam’iyyu sama da 40 a kasar nan, jam’iyyar da ke da babban rinjaye a majalisun dokokin jihohi da majalisar wakilai ta tarayya da kuma majalisar dattawa ta kasa.
To, duk da wannan karfi da girma da daukaka da wannan jam’iyyar ta ke da shi, sai ga shi kuma dare da rana tana ta kyarkyarar mutane da jam’iyyun adawa da sunan kafa gwamnatin hadin kai da neman gafara da sasantawa. Abin da ya kwance mani kai shi ne wace sasantawa? Wace gafara? Wace gwamnatin hadin kai?
Wadannan tambayoyi za su yi saukin amsawa idan har muka yi cikakken nazari wannan yanayi da halin da jam’iyyar da gwamnatinta ta ke ciki a halin yanzu.
Tun ranar 29 ga watam Mayun wannan shekarar lokacin da aka rantsar da Alhaji Ummaru Musa ‘Yar adua a matsayin shugaban kasa ya bayyana cewa zaben da aka yi fa yana da gyara kuma zai yi kokari ya ga cewa ya gyara duk wata matsala da aka samu. To, da alama wannan shi ne ya sanya wannan jam’iyya da gwamnatin ‘Yar adua suka dukufa wajen wannan sabon aiki ko jan aiki da suka dorawa kansu. A zaton su a iya sasantawa saboda duk wadanda aka yi wa ba daidai ba, tun da sun san PDP ta kafa gwamna za su yarda a sasanta, wasu daga cikin su ma, ai za su kawo kansu suna neman gafara don a ba su mukamai. Sai dai kuma a zahirin gaskiya ko kusa wannan al’amarin ba haka yake ba, domin ba yadda za a yi ka kwance wa mutun zani a kasuwa daga baya ka ce da shi ya yi hakuri za ka daura masa. To, sai dai idan daman can shi wanda aka kwance wa zanen a kasuwa, dan tashar ko kuma ba mai yin siyasar ne da akida da alkibla ba. Idan haka ne kuwa to, tir da mai siyasar son kai da neman kudi. Tir da mai siyasar ‘nawa zan samu, ba wace irin gudunmuwa zan bayar wajen ci gaban al’umma ta ba.’ Tir da mai siyasar ‘idan na samu to, kowa ma ya rasa!’
Saboda haka ni a nawa ra’ayi tuni an rigaya an bar kyawo tun ranar haihuwa, don haka ba wata sasantawa da za a yi da jam’iyyar PDP, hasali ma duk wani da muka ga ya sake koma PDP mun san manufarsa da tunaninsa da wayonsa da dabararsa, saboda haka za mu sa shi a ranmu mu kiyaye da shi mu tabbatar da cewa muna nan hake da shi kuma sai mun rama, idan ba yanzu ba, to, an jima ko gobe ko jibi ko nan gaba ko ma wata rana. Ba za mu sake mu bari ya yi tasiri a siyasar kasar nan ba, za mu tabbatar da cewa mun kai shi kasa duk lokacin da kaddara ta ingiza shi ya shiga zabe. Wannan ke nan!
To, wace gafara kuma? To, ai sai idan mutum ya amince da laifinsa, sa’ilin nan za a gafarta masa ko a yafe masa, ko baya ga wannan ai sai idan ya amince da cewa lallai ba zai sake aikata irin wannan laifi ba. To, amma mutanen nan da suka ce a gafarta masu, har gobe muna kotu da su, kuma sun dauki lauyoyi domin a ba su kariya a bayyanawa kotu da duniya cewa ba su aikata wannan laifi ba. To, idan har suna neman gafara, kamata ya yi su sauka daga mukamansu, su amince da laifukansu su kuma yarda a sake sabon zabe! Idan har suka yi haka mun tabbatar da cewa sun yarda da laifin su, suna neman gafara mu kuma ba shakka za mu yafe masu.
A gani na bai kamata a ce jam’iyyar da ke ikirarin cewa ita ce ke da karfi, ita ce ke da mulki, ita ce ke da kudi, ita ce ke da komai da komai kuma a ce ta dawo ta bayan gida tana kame-kame ba!