Sunday 19 August 2007

Me PDP Ke So?

PDP fawa!, PDP fawa!!, Wannan shi ne kirarin jam’iyyar PDP, jam’iyyar siyasa mafi girma a nahiyar Afurka! Haka ne mana, domin kullum haka suke fada! Ita dai jam’iyyar PDP, ita ce ke jan ragwamar mulkin gwamnatin tarayyar Nijeriya da kuma mafi rinjayen jihohi 36 a Nijeriya. Jam’iyya ce da ta hada tsofaffi da sababbin jinin ‘yan siyasa, jam’iyya ce da ke alfahari da tattara tofaffi da kuma manyan sojojin da ma tsofaffin shugabannin kasar nan. PDP ke nan, jam’iyyar da ta taushe sauran kananan jam’iyyu sama da 40 a kasar nan, jam’iyyar da ke da babban rinjaye a majalisun dokokin jihohi da majalisar wakilai ta tarayya da kuma majalisar dattawa ta kasa.
To, duk da wannan karfi da girma da daukaka da wannan jam’iyyar ta ke da shi, sai ga shi kuma dare da rana tana ta kyarkyarar mutane da jam’iyyun adawa da sunan kafa gwamnatin hadin kai da neman gafara da sasantawa. Abin da ya kwance mani kai shi ne wace sasantawa? Wace gafara? Wace gwamnatin hadin kai?
Wadannan tambayoyi za su yi saukin amsawa idan har muka yi cikakken nazari wannan yanayi da halin da jam’iyyar da gwamnatinta ta ke ciki a halin yanzu.
Tun ranar 29 ga watam Mayun wannan shekarar lokacin da aka rantsar da Alhaji Ummaru Musa ‘Yar adua a matsayin shugaban kasa ya bayyana cewa zaben da aka yi fa yana da gyara kuma zai yi kokari ya ga cewa ya gyara duk wata matsala da aka samu. To, da alama wannan shi ne ya sanya wannan jam’iyya da gwamnatin ‘Yar adua suka dukufa wajen wannan sabon aiki ko jan aiki da suka dorawa kansu. A zaton su a iya sasantawa saboda duk wadanda aka yi wa ba daidai ba, tun da sun san PDP ta kafa gwamna za su yarda a sasanta, wasu daga cikin su ma, ai za su kawo kansu suna neman gafara don a ba su mukamai. Sai dai kuma a zahirin gaskiya ko kusa wannan al’amarin ba haka yake ba, domin ba yadda za a yi ka kwance wa mutun zani a kasuwa daga baya ka ce da shi ya yi hakuri za ka daura masa. To, sai dai idan daman can shi wanda aka kwance wa zanen a kasuwa, dan tashar ko kuma ba mai yin siyasar ne da akida da alkibla ba. Idan haka ne kuwa to, tir da mai siyasar son kai da neman kudi. Tir da mai siyasar ‘nawa zan samu, ba wace irin gudunmuwa zan bayar wajen ci gaban al’umma ta ba.’ Tir da mai siyasar ‘idan na samu to, kowa ma ya rasa!’
Saboda haka ni a nawa ra’ayi tuni an rigaya an bar kyawo tun ranar haihuwa, don haka ba wata sasantawa da za a yi da jam’iyyar PDP, hasali ma duk wani da muka ga ya sake koma PDP mun san manufarsa da tunaninsa da wayonsa da dabararsa, saboda haka za mu sa shi a ranmu mu kiyaye da shi mu tabbatar da cewa muna nan hake da shi kuma sai mun rama, idan ba yanzu ba, to, an jima ko gobe ko jibi ko nan gaba ko ma wata rana. Ba za mu sake mu bari ya yi tasiri a siyasar kasar nan ba, za mu tabbatar da cewa mun kai shi kasa duk lokacin da kaddara ta ingiza shi ya shiga zabe. Wannan ke nan!
To, wace gafara kuma? To, ai sai idan mutum ya amince da laifinsa, sa’ilin nan za a gafarta masa ko a yafe masa, ko baya ga wannan ai sai idan ya amince da cewa lallai ba zai sake aikata irin wannan laifi ba. To, amma mutanen nan da suka ce a gafarta masu, har gobe muna kotu da su, kuma sun dauki lauyoyi domin a ba su kariya a bayyanawa kotu da duniya cewa ba su aikata wannan laifi ba. To, idan har suna neman gafara, kamata ya yi su sauka daga mukamansu, su amince da laifukansu su kuma yarda a sake sabon zabe! Idan har suka yi haka mun tabbatar da cewa sun yarda da laifin su, suna neman gafara mu kuma ba shakka za mu yafe masu.
A gani na bai kamata a ce jam’iyyar da ke ikirarin cewa ita ce ke da karfi, ita ce ke da mulki, ita ce ke da kudi, ita ce ke da komai da komai kuma a ce ta dawo ta bayan gida tana kame-kame ba!