Monday 29 October 2007

Daga kin gaskiya...

Daga
Isah M. Bello Na’iyya

Ban cika son in tabi abinda ya shafi jama’a ba, don gudun kar in yi wa wani ba daidai ba, amma kuma duk da haka, da yake masu magana na cewa gyara kayanka bai zama sauke mu raba, ina ganin tilas in ce wani abu.
Hausawa ke cewa, daga kin gaskiya sai bata, mai karatu, sanin ka ne cewa duk fa yadda aka narka karfe sunansa karfe, na fahimci saboda haka ne ma ake kwatanta gaskiya da dokin karfe, ko tana gudu kama ka haye, ba ka faduwa insha Allahu.
Dukkan lamari ko sha’anin da mutum zai aikatawa a rayuwarsa, indai yana bukatar ci gaba da kuma nasara, to tilas sai ya gama da gaskiya. Gaskiya ita ce takobin yakin duk wani lamari na rashin gaskiya ko yaudara ko zalunci ko ha’inci da ya addabi jama’a.
Babu wai wai, domin gaskiya ita ce addinin mutum, kuma da ita ce bawa zai yi godogo ko tinkaho, har ya zuwa karshen rayuwarsa. Bari in baka misali, - idan kai dan kasuwa ne ko ma’aikacin gwamnati, mai mulki ne kai ko mai sarauta, kai attajiri ne ko talaka, kai ko ma dai wane irin matsayi ka tsinci kanka a rayuwarka ta duniya, sai ka zamo mai gaskiya sannan mutane za su soma tunanin cewa kai mutum ne kammalalle kuma mai ma’ana, mai adidni, gwarzo kuma haziki.
Gaskiya ce kurum za ta iya sanya ka zamo sananne a cikin al’umma wanda kuma ake alfahari da shi. Kar ka manta da duk lokacin da gaskiyar mutum ta yi kadan to fa tabbas abokan huldarsa ma za su yi karanci.
Kar kuma ka manta duk fa wanda karya ta hada ku, to gaskiya za ta raba ku, amma idan gaskiya ce ta hada ku, to karya ba ta isa ta raba ku ba. sau da yawa rayuwarka za ta baci idan kuna magana da wani, to sai dai kuma kai tsaye kana iya fahimtar cewa gaskiya ce yake fada ma domin maganar gaskiya ba ta yi kama da kowace irin magana ba.
Haka kuma, a duk lokacin da aka fada ma maganar gaskiya, ka daure ka dauke ta ke kuma kar~eta hannu biyu, ka yi aiki da ita, insha Allahu za ka ji da]in tafiyar da rayukarka. Kowane al’amari yana karfafa ne idan aka yi aiki da gaskiya a cikinsa.
Dan uwa, mai karatu, ka taba aikata gaskiya? An taba yin aikin gaskiya a tare da kai? Ka taba ganin mutumin da gaskiyar sa ta kare? Ka taba jin kana kyamar mutumin da ke fadin gaskiya? Da yawa na san akwai dimbin tambayoyin da watakila za ka iya amsawa a game da kanka a kan mai gaskiya da maras gaskiya.
Hausawa kan yi wa gaskiya kirari iri-iri kamar: gaskiya mai daci, gaskiya ba ta neman ado, gaskiya matakin nasara, gaskiya dokin karfe, gaskiya mai dadi ko an ki ta ana ganin ranar ta, kowa ya ki gaskiya rabo nai kunya, in za ka fadi fadi gaskiya, komai ta ka ja maka ka biya.
Lokaci da yawa fadin gaskiya, yakan jayo wa mutum fitina, amma in ya yi hakuri zai ga amfanin fadin gaskiyar ko da kuwa akan sa ne.
Bari in baka wani dan takaitaccen labari game da wani bawan Allah, wanda labari ne mai karantarwa.
Wata rana wani bawan Allah yana cikin karantarwa a kofar gidansa, sai ga wani barawo a guje, yana gudu yana neman agaji daga wadanda suka biyo shi, yana zuwa wurin wannan bawan Allah, sai ya ce don Allah Malam ka taimake ni ka da su kashe ni, sai malamin ya ka da baki ya ce, ga wundi nan ka dauka ka boye kanka, barawon kuwa bai yi wata-wata ba ya dauki wundin ya zagayawa kansa ya boye, can kuma sai ga wadanda suka biyo shi, su ma suna zuwa sai suka cewa malamin don Allah malam barawo ne muka biyo ya bace muna, don Allah ina ka ga ya bi sai Malamin ya ce ga shi nan cikin wundi, nan take mutanen suka fusata suka yi gaba suna fada suna cewa ya ya za mu ce ma muna neman barawo ka ce wai ga shi nan cikin wundi, wane irin wundi? Bayan sun wuce sai barawon ya fito daga cikin wundin yana cewa hakika ko gobe gaskiya na aiki, kuma tun daga wannan lokacin barawon nan bai sake yin sata ba.
Dan uwa mai karatu, idan har za ka yi duba mai kyau na nazari, to, za ka fahimci cewa addinin Musulunci ma an gina shi baki dayan sa a kan gaskiya. A duk tsawon rayuwarka kuwa, matukar aka san ka da rashin gaskiya to, a wasu lokuta ko da gaskiya ka yi ba a yarda da kai.
A cikin Alkur’ani Mai girma, Allah Madaukakin Sarki Yana cewa, “ku fadi gaskiya daga Ubangijinku, amma idan kuka ga dama ku yi imani, idan kuka ga dama ku kafirce.”
A wata ayar kuwa Allah Yana cewa, “ya ku wadanda suka yi imani, ku ji tsoron Allah ku kasance masu gaskiya.”
A cikin wani Hadisi, Manzon Allah (SAW) ya na cewa, ita gaskiya tana shiryawa zuwa ga aljanna. Har wa yau dai Manzon Allah (SAW) yana cewa a cikin wani hadisi, cewa “na hore ku da yin gaskiya, hakika ita gaskiya tana tare da da’ar Allah dukkan su kuma suna kai mutum aljanna.”
Allah ya taimakemu mu zamao masu gaskiya amin summa amin.

No comments: